Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Majalisar dokokin Kano ta gayyaci Muhuyi Magaji da ya bayyana a gabanta

Published

on

Majalisar dokokin Kano ta gayyaci dakataccen shugaban hukumar karbar korafi da yaki da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado, domin fuskantar bincike kan korafin da akanta janar na Jihar ya shigar gabanta.

Wasikar gayyatar na dauke da sa hannun sakataren kwamitin kula da harkokin shari’a na majalisar Abdullahi Bature, wadda ta bukaci Muhuyi Magaji da ya bayyana gaban majalisar a gobe Laraba 14 ga watan Yuli da karfe 12 na rana.

Haka zalika wasikar ta bukaci Muhuyi Rimin Gado ya yi mata cikakken bayani kan kudaden da ya kwato daga shekarar 2015 zuwa lokacin da aka dakatar da shi.

Baya ga wannan, majalisar ta bukaci ya gabatar mata cikakkun bayanan hada-hadar kudaden da aka gudanar a hukumar, da suka hadar da gudunmawar da ta karba a hukumomi daban-daban tun daga shekarar 2015 zuwa yanzu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!