Labarai
Amnesty International ta bukaci a kawo ƙarshen ayyukan ’yan ta’adda a Jihar Zamfara

Kungiyar Kare Haƙƙin Dan Adam, ta Amnesty International ta bukaci da a kawo ƙarshen ayyukan ’yan ta’adda a Jihar Zamfara, da ta ce rashin tsaro ya janyo asarar daruruwan rayuka tun daga shekarar 2012 zuwa yanzu.
Ta cikin sanarwar da kungiyar ta fitar, a Daren jiya Asabar Amnesty ta ce hare-haren da ake kai wa al’umma sun jefa kauyuka da dama cikin halin kunci.
Sanarwar ta ce mazauna kauyuka kan samu gargadi kafin kai hari, ciki har da kiran waya da ake bukatar su biya kudade ko su fuskanci kisa ko garkuwa, da maharan kan kai hari domin sace ’yan mata da dabbobi.
Kungiyar ta kuma ce daruruwan kauyuka a kananan hukumomi 13 daga cikin 14 na jihar sun zama kufai bayan hare-haren, lamarin da ya sa mutane da dama suka rasa muhallan su.
Amnesty, ta bukaci hukumomin ƙasar nan su dauki matakan gaggawa domin kare rayukan jama’a tare da gurfanar da wadan da ake zargi a gaban kotu bisa ka’ida, don girbar abinda suka shuka.
You must be logged in to post a comment Login