Labarai
Amnesty ta buƙaci shugaba Tinubu ya kawo ƙarshen kashe-kashen mutane a Zamfara

Ƙungiyar kare hakkin Dan-adam ta Amnesty International, ta buƙaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, da ya tabbatar an kawo ƙarshen kashe-kashen mutane da ke faruwa a jihar Zamfara.
Amnesty ta faɗi hakan ne a matsayin martani kan rahotannin kisan da ƴan fashin daji suka yi wa mutane aƙalla 38 da suke garkuwa da su a ƙaramar hukumar Ƙauran Namoda.
Sanarwar da Amnesty ta fitar a shafinta na X, ta ce “babu wani yanki na Zamfara da ke cikin aminci tun daga shekarar 2018.
Sanarwar ta ƙara da cewa “ƴan fashin daji sun kori ƙauyuka 481 tun farkon matsalar, sannan akwai ƙauyuka 529 na ƙananan hukumomi 13 na jihar da ke ƙarƙashin ikon ƴan fashin dajin.”
You must be logged in to post a comment Login