Connect with us

Labarai

Amnesty ta bukaci a gudanar da bincike kan kisan matafiya a Filato da harin Adamawa

Published

on

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta kasa da kasa  ta Amnesty International, ta bukaci hukumomin Najeriya da su gudanar da bincike kan kisan matafiya a Jihar Filato da kuma harin da ya yi sanadin mutuwar sama da mutane 24 a a Jihar Adamawa.

 

Amnesty International reshen kasar nan   ta bayyana hakan cikin sanarwa da ta fitar jiya Laraba.

 

Kungiyar ta ce an kashe mutane hudu bayan wasu dauke da makamai suka tare hanya tare da kai hari kan matafiya a yankin Ninigi na Karamar Hukumar Barkin Ladi ta Jihar Filato, lamarin da ya biyo bayan harin ramuwar gayya da ya yi sanadin mutuwar mutane bakwai a kauyen Dorawa Babuje.

 

Kungiyar  ta ce sama da mutane 24 sun rasa rayukansu yayin da dama suka jikkata sakamakon harin da aka kai a kauyukan.

 

Amnesty ta nuna cewa irin wadannan hare-hare na kara barazana ga rayuwa da ‘yancin zirga-zirga, tare da kira ga hukumomi su dauki matakan kare al’umma da kuma hukunta wadanda ake zargi da hannu a hare-haren.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!