Labarai
Shugaba Tinubu ya bada umarnin yin bincike kan kashe-kashen Filato

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna takaicinsa tare da bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike bisa harin da wasu bata gari suka sake kai wa jihar Filato wanda ya yi sanadiyar hallaka mutane fiye da 40.
Wata sanarwar da mai magana da yawun shugaban Bayo Onanuga ya fitar ta ruwaito cewa, shugaba Tinubu ya aike da sakon jaje ga gwamnatin Jihar ta Filato da kuma al’ummar jihar, tare da bada umarnin daukar matakan da suka dace wajen warware rikicin da kuma samar da dauwamammen zaman lafiya.
Haka kuma, shugaban ya bukaci gwamnnan Jihar Caleb Mutfwang da ya dauki matakin magance matsalar da ake samu ta yawan kashe-kashen mutane.
Haka kuma, Shugaban kasa Tinubu, ya bukaci shugabannin addinai da na siaysa a ciki da wajen jihar da su hada kai wajen kawo karshen irin wadannan hare-hare da kuma daukar fansa, wadanda ke jefa al’ummomi cikin tashin hankali.
You must be logged in to post a comment Login