Connect with us

Labarai

Amnesty ta zargi gwamnatin Tinubu da gaza kare rayukan yan Najeriya

Published

on

Kungiyar kare hakkin Dan-adam ta Amnesty International, ta zargi gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu da gaza kare rayukan ‘yan Najeriya.

Wsannan zargi dai na zuwa ne bayan da rahotonni suka bayyana cewa ‘yan bindiga sun kashe fiye da mutane ashirin a wani kauye da ake hakar ma’adinai a jihar Zamfara. 

Wata sanarwa ta Daraktan kungiyar ta Amnesty International a Najeriya, Malam Isa Sanusi, ya fitar ta ce, akalla mutane hamsin da hudu  aka kashe a hare-hare daban-daban a ‘yan  kwnakin nan.

A makonnin baya-bayan nan ne ‘yan bindiga suka rika kai hare-hare tare da kashe mutane da kona gidaje da amfanin gona a jihohin Benue da Plateau.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!