Ƙetare
Amurka ta tabbatar da kama shugaban ƙasar Venezuela

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya ce ƙasarsa ta ƙaddamar da wani ”mummunan hari kan Venezuela” tare da “kama shugaban ƙasar, Nicolas Maduro” da matarsa.
Cikin wani gajeren saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, shugaban na Amurka ya ce a lokacin harin an kama Shugaba Maduro da matarsa tare da ficewa da su daga ƙasar.
Mista Trump ya ce an ƙaddamar da harin ne tare da haɗin gwiwar jami’an Amurka.
Dama dai Amurka ta jima tana barazanar kai hari Venezuela sakamakon tsamin dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu, wanda ya biyo bayan zaɓen shugaban ƙasar da ya gabata.
You must be logged in to post a comment Login