ilimi
An bai wa jami’o’I masu zaman kansu guda 20 lasisi
Gwamnatin Tarayya ta gabatar da lasisi ga sabbin jami’o’i masu zaman kansu 20 da majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da su a kwanakin baya.
Lasisin wanda aka gabatar wa jami’o’in a Alhamis din nan a Abuja, ya kawo jimillar jami’o’in masu zaman kansu a kasar nan sun kai 99.
Majalisar zartarwa ta tarayya a watan Fabrairun 2021, ta amince da kafa sabbin jami’o’i masu zaman kansu guda 20.
Da yake jawabi a wajen taron, Ministan Ilimi Adamu Adamu ya ce amincewar kafa wadannan jami’o’i wata manuniya ce ga ci gaban kawancen da gwamnatin tarayya ke yi da kamfanoni masu zaman kansu wajen fadada harkokin ilimin jami’o’i a Najeriya.
Ministan wanda Karamin Ministan Ilimi Emeka Nwajiuba ya wakilta, ya ce Najeriya na bukatar karin jami’o’i duba da yawan al’ummar kasar.
Adamu Adamu ya ce, tare da yawan jama’ar kasar, yawan jami’o’in da ke yanzu ba su da yawa idan aka kwatanta da na sauran kasashe kamar Brazil, Mexico da Rasha.
You must be logged in to post a comment Login