Connect with us

Labarai

An bindige ƙasurgumin ɗan fashi a jihar Zamfara

Published

on

An harbe ƙasurgumin ɗan fashin nan da ke satar mutane har ma da shanu mai suna Damuna a jihar Zamfara.

Kungiyar da Dogo Gide ke jagoranta ce ta kashe Damina a wata arangama.

Damuna ya daɗe yana aikata ta’addanci a jihar Zamfara musamman a dajin ƙuyanbana da ke masarautar Ɗansadau a ƙaramar hukumar Maru.

Jaridar DailyTrust ta rawaito cewa a watan Yulin da ya gabata Damina ya kai hari a ƙauyukan Tungar Baushe da Randa, inda ya kashe mutane da dama tare da yin garkuwa da wasu mazauna yankin fiye da 100 galibi mata da ƙananan yara.

Wata majiya ta ce Dogo Gide, ana kyautata zaton yana da alama da ISWAP, ya kai wa Damina farmakin tare da bindige shi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!