Connect with us

Labarai

An boye daliban Kagara a Birnin Gwari – Matawalle

Published

on

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya ce dalibai da ma’aikatan Kwalejin Kimiyya da ke Kagara a jihar Neja da ’yan bindiga suka sace a ranar Laraba da ta gabata suna tsare a Birni Gwari dake jihar Kaduna tare da wadanda suka sace su.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a shirin Talabijin na Channels yana mai tabbatar da cewa nan ba da jimawa ba za a saki wadanda aka sace.

Matawalle ya yi zargin cewa akwai hadin kai daga masu ruwa da tsaki wajen aikata miyagun laifi, wanda shi ne ya ke bai wa yan ta’addar nasara a cikin ayyukan da suke yi na ta’addanci a ƙasar nan.

A cewarsa, batun tsaro na bukatar karin himma daga dukkan masu ruwa da tsaki musamman na magance matsalolin ayyukan yan Boko Haram da masu garkuwa da mutane.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,961 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!