Connect with us

Labarai

 Fulani mutane ne masu son zaman lafiya – Yuguda

Published

on

Tsohon gwamnan jihar Bauch Malam Isah Yuguda ya yai Allah wadai da alakanta Fulani da ayyukan ta’addanci da ake yi a wannan lokaci.

Isah Yuguda ya bayyana hakan ne jim kadan bayan sabunta rijisatr sa ta zama dan jam’iyyar APC.

Ya ce, a yanzu ana mu’amalantar Fulani ta wani bangare daban tare da yi musu kallo na mutane marasa son zaman lafiya wanda kuma hakan ya sabawa halayya ta Fulani.

Yuguda ya kuma ce Fulani mutane ne da suke samarwa Najeriya abubuwan more rayuwa amma duk da haka gwamnati bata basu kulawar da ta kamata.

A cewarsa matukar gwamnati za ta iya sakin kudade masu yawan gaske don tallafin noma mai yasa ba za ta bai wa Fulani tallafi wajen inganta harkokin kiwon su ba.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,961 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!