Labarai
An bukaci Kanikawa da su sanya tsoron Allah a aikin su
Hadaddiyar kungiyar Kanikawa ta kasa mai suna (GATAN) ta bukaci ‘ya’yanta da su kasance masu gaskiya da rikon amana a yayin gudanar da sana’arsu wanda hakan zai taimaka wajen samar da alaka mai kyau tsakanin su da abokan huldar su.
Shugaban kungiyar ta GATAN kwamared Idris Muhammad Kanwa ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da Freedom Radio.
Kwamared Idris Muhammad Kanwa ya ce sanya gaskiya da tsoron ubangiji yayin gudanar da aikin zai taimaka wajen inganta sana’ar ta Kanikanci.
Ya kara da cewa kungiyar su ta na iya kokarin ta wajen ganin ta hada kan ‘ya’yan ta a duk inda suke, tare inda ya bayyana cewa hakan zai taimaka wajen saukaka sana’ar tare da bunkasa tattalin arzikin masu gudanar da ita.
Wakilinmu Shamsu Da’u Abdullahi ya ruwaito Shugaban kungiyar ta GATAN kwamared Idris Muhammad Kanwa na cewa sana’ar Kaninkanci sana’a ce mai sauki tare da samar da rufin asiri, inda ya bukaci matasa da su rungumi wannnan sana’a, yana mai cewa zata taimaka kwarai da gaske wajen rage matsalar rashin aikin yi a tsakanin matasa.