Connect with us

Ƙetare

An daga ranar yin jana’izar Marigayi Aminu Dantata

Published

on

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana’izar fitaccen ɗan kasuwar Alhaji Aminu Dantata daga yau Litinin zuwa gobe Talata.

 

Ministan yaɗa labaran Najeriya, Mohammed Idris ya tabbatar wa da BBC ɗage jana’izar sakamakon rashin isar gawar marigayin a kan lokaci zuwa birnin Madina.

 

Ministan ya ce Akwai ƙa’idoji da gwamnatin Saudiyya ta shimfiɗa kan yadda za a shigar da gawa domin yi mata jana’iza a ƙasar,  da ake ci gaba daa cike-ciken takardu tsakanin gwamnatin Saudiyya da iyalan mamacin.

 

Mohammed Idris ya ce idan an kammala za a ɗauko gawar daga Hadaɗɗiyar Daular Larabawa zuwa Saudiyya, da ya ƙara da cewar  tuni ofishin jakadancin Najeriya a Saudiyya da iyalan mamacin suka kammala shirye-shiryen jana’izar.

 

Tun da safiyar yau Litinin ne tawagogin gwamnatin tarayya da na gwamnatin jihar Kano suka tafi Saudiyyar da nufin halartar jana’izar da aka shiryi yi a yau Litinin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!