Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An dage zaben mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na Arewa maso Yamma

Published

on

Babbar jamiyar adawa ta kasa wato PDP ta dage gudanar da zaben mataimakin shugaban ta na Arewa maso Yammacin kasar nan.

Sakataren yada labaran kwamitin gudanar da zaben Dakta Abdurrahman Usman, ya shaidawa Freedom Radio cewa an dage zaben ne saboda rashin cikakkun takardun zabe.

Inda yace nan gaba kadan zaa sanya ranar da za’a gudanar da zaben.

sai dai rahotanni sun tabbatar da cewa rikici ya barke tsakanin wakilan jam’iyyar daga Kano, lamarin da ya sanya aka dage zaben.

Idan za’a iya tunawa dai a yau Asabar jamiyar ta PDP ta shirya gudanar da zaben, inda kuma rahotannin da sukai ta fita a jiya juma’a suka nuna akwai sa-in-sa tsakanin jagoran kwankwasiya injiniya Rabiu Musa Kwankwaso da gwamnan jihar Sokoto Alhaji Aminu Waziri Tambuwal akan wadanda za su fito takarar neman zama mataimakin shugaban jamiyar mai kula da Arewa maso Yamma.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!