Labarai
An daura auren Sadiya Farouq da Air Marshal Sadiq Abubakar
A karshen makon da ya gabata ne aka daura auren Babban hafsan sojin saman kasar nan Air Marshal Sadiq Abubakar da minstar al’amuran jinkai da kare afkur iftila’I da ci gaban al’umma Hajiya Sadiya Umar Farouq.
A dai ranar goma sha Takwas ga watan Satumbar da muke ciki ne aka daura auren a masallacin Juma’a da ke Maitama a birnin Tarayya Abuja.
Wata majiya ta shaidawa jaridar Daily Trust cewa mutane kalilan ne suka hallarci daurin Auren da aka gudanar.
A dai shekarar ta dubu biyu biyu da goma sha tara ne aka dinga yada jita jita cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai auri Misitan al’amuran jin kai da kare afkur iftila’I Hajiya Sadiya Umar Farouq.
A dai kwanakin baya ne fadar shugaban kasa ta maida martani kan zargin da wasu ke yi cewa Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta yi yaji.
A cewar fadar shugaban kasar Aisha Buhari na da ‘yancin tafiya duk in da take son zuwa, kuma bata yi rikici da kowa ba a fadar shugaban kasar dake Abuja.
Bayanin haka ya fito ne ta bakin mai Magana da yawun ta Suleman Haruna ‘’cewa watannin 2 da ba’a ganin fuskar uwargidan shugaban kasar, ba yana nufin cewar babu fahimtar juna a tsakanin ta da maigidan ta ba ko kuma wasu jiga-jigan gwamnati mai ci’’a’a illa kawai wasu ne ke kitsa labarun karya don tada fitina’’
Rahotanni sun bayyana cewar fadar shugaban ta tabbatar da cewar uwargidan shugaban kasar ba ta kasar nan, amma kuma ba yaji tayi ba,illa kawai kowannne dan adam na da uziri kamar kowa a don haka babu zancen cewa tana da ‘yar tsama da shugaban kasa da kuma makarraban sa.
Sai dai idan aka gayyaci Aisha Buhari babbar mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin sha’anin mulki Dr, Hajo Sani na wakiltar ta, ciki har da taron kungiyar cigaban matan shugabannin kasa na kashashen Afrika wanda aka yi a ranar 25 ga watan nan da muke ciki karo na 74 wanda yake cikin kunshin babban zauren taron majalisar dinkin duniya da aka yi birnin New York.
You must be logged in to post a comment Login