Connect with us

Labarai

An dawo da sufurin jiragen kasa bayan samun tangarda a titin Kaduna zuwa Abuja

Published

on

Hukumar kula da sufurin jiragen kasa a Najeriya NRC ta sanar da cewa an dawo da zirga-zirgar jiragen ƙasa tsakanin Abuja da Kaduna gaba ɗaya bayan tangardar da aka samu a farkon mako. Manajan Daraktan hukumar, Kayode Opeifa, ya bayyana hakan, yana mai tabbatar wa fasinjoji cewa an ɗauki sabbin matakan tsaro da inganta aiki domin tabbatar da tafiya cikin aminci da kwanciyar hankali.

Ya ce an samu wannan nasara ne sakamakon saurin ɗaukar mataki da hukumar ta yi bayan lamarin da ya faru ranar 16 ga Maris, 2026. Haka kuma, ya bayyana cewa jirgin da ke jigila daga daga Rigasa a Jihar Kaduna ya riga ya fara aiki yadda ya kamata, wanda ke nuna komawar al’amura yadda suke a baya ga masu amfani da layin jirgin.

Tun da farko dai, an samu matsalar ne kusa da tashar Asham, inda wani ɓangare na jirgin ya rabu yayin tafiya sannan ya koma baya ya buge sauran jirgin. Jirgin na ɗauke da fasinjoji 429 tare da ma’aikata

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!