Connect with us

Labarai

Hukumar jiragen kasa ta kasa ta nemi afuwan fasinjoji

Published

on

Hukumar jiragen kasa ta kasa ta bayyana damuwarta da rashin jin dadin ta sakamakon rashin tashi da  jirgin yayi a ranar talatar da ta gabata kamar yadda aka tsara wanda zai dauki fasinja daga Abuja zuwa Kaduna.

Mataimakin daraktar  sashin yada labarai Mal Yakub Moahmood ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar jiya ga kamfanin dillancin labarai.

Ya ce hukumar ta bayyana rashin jin dadinta na rashin aiki da jirgin yayi a ranar talatar da ta wuce, inda aka samu matsala daga tashar ta Rigasa dake jihar Kaduna.

Katsina:wani jirgin shalkwabta rundanar sojin kasar nan yayi hadari

Farfelar jirgin saman rundanar sojin kasar nan ya fille kan want hafsan sojin sama

Najeriya ta rasa yan kasar ta guda biyu a hatsarin jirgin saman kasar Ethopia

Hukumar ta nemi afuwa dukkanin fasinjojin na faruwar hakan, tare da neman afuwarsu.

Mahmood ya kara da cewa tuni aka magance matsala kuma jiragen suka fara aiki yadda ya kamata

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 335,225 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!