An Tashi Lafiya
An fara rushe shagunan sayar da magunguna marasa inganci a Jihar Adamawa
Hukumar kula da sha’anin sarrafa magunguna PCN, reshen jihar Adamawa ta gudanar da wani bincike a ƙananan hukomi, kan waɗanda suka karya ƙaidojin hukumar ta hanyar rufe shagunan sayar da magunguna a Jihar.
Hakan ya biyo bayan wani sumame da jami’an hukumar suka fara, na tantance masu sayar da magunguna tare da ingancin su.
Emmanuel Egwu, mataimakin darakten hukumar kuma jami’in dake kula da jihar kan fannin sarrafa magunguna ya bayyanawa Freedom Radio cewa bayan an bawa mutum damar sayar da magani akwai buƙatar a rinƙa bibiyar al’amuran sa domin ganin abinda ya keyi.
Ya kuma ƙara da cewa “mun rufe shagunan waɗanda ake tuhuma da aikata laifuka, za kuma mu gurfanar da wasun su a gaban shari’a, domin babu wanda aka bawa damar sayar da magunguna ba tare da takardar shaida ba. Aikata hakan, laifi ne da ka iya jawo aci taron naira dubu dari biyar da kuma zaman yari har na tsawon shekaru biyu.”
You must be logged in to post a comment Login