Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An fara yunƙurin tsige mataimakin Gwamnan Zamfara

Published

on

Majalisar dokokin jihar Zamfara na shirin tsige mataimakin Gwamnan jihar Barista Mahdi Ali Gusau.

Wannan dai ya biyo bayan zarginsa da wasu laifuka guda takwas da kundin tsarin mulkin ƙasa ya amince a tsige me irin wannan laifukan.

Shugaban majalisar dokokin jihar Nasiru Ma’azu Magarya ne ya bayyana haka a lokacin da yake yiwa wakilin Freedom Radio Yusuf Ibrahim Jargaba ƙarin bayani.

Ya ce “Yau da safe ƴan majalisar sun gabatar da takarda kan buƙatar su ta a tsige mataimakin Gwamnan, kuma na karɓi takardar”.

“Za mu zauna mu yi nazari kafin mu aiwatar da hukunci na gaba” a cewar Magarya.

Ana zargin hakan na da nasaba da ƙin komawar mataimakin gwamnan zuwa jam’iyyar APC bayan da Gwamna Bello Matawalle ya bar jam’iyyar PDP ya koma APC.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!