Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yadda zaman shari’ar Abduljabbar ke kasancewa

Published

on

Yau ne ake sa ran Malam Abduljabbar zai fara kare kansa bisa tuhumar da ake masa.

Babbar kotun Shari’ar musulunci mai zamanta a ƙofar kudu ƙarƙashin jagorancin mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ta fara sauraron shaidun kariya a ƙunshin tuhumar da gwamnatin jihar Kano ke yiwa malamin.

Tuni dai kotun ta zauna da safiyar yau Alhamis wanda kuma Lauyansa Malami A. O Muhammad (SAN) ya roƙi Kotu ta dawo da shaida na farko da na biyu domin sake yi musu tambaya.

Wakilan Freedom Radio da ke kotun Yusuf Nadabo Ismail da Aminu Abdu Baka Noma sun rawaito cewa an jibge tarin jami’an tsaro a harabar kotun.

Idan za a iya tunawa ana dai zargin malam Abduljabbar da laifin ɓatanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammadu zargin da malamin ya musanta, a zaman kotun na yau Alhamis.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!