Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kasuwanci

An gano arzikin zinare mai yawa a Nigeria- Buhari

Published

on

Gwamnati tarayya ta ce ta gano dumbin arzikin ma’adinan zinare a wani yanki da ke tsakanin birnin tarayya Abuja da jihar Nassarawa.

Ministan tama da karafa Olamilekan Adegbite ne ya bayyana haka lokacin da ya ke ganawa da gwamnan jihar Nassarawa Abdullahi Sule wanda ya kai masa ziyara ofishinsa da ke Abuja.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun ministan, Ayodeji Adeyemi, ta ruwaito mista Adegbite na shaidawa gwamnan cewa, gwamnatin tarayya tana shirye-shiryen neman hanyoyin da za ta bi don a fara cin gajiyar arzikin.

‘‘Muna ta shirye-shirye ne don ganin mun samu sahihan hanyoyi da suka kamata kafin fara cin gajiyar arzikin zinaren, saboda mun dauki darussa masu yawa kan halin da ake ciki a jihar Zamfara’’ a cewar mista Adegbite.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!