Connect with us

Labarai

Dalilan da suka sanya Buhari ya ce gwamnatoci ba zasu iya sarrafa ma’adanai ba

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce gwamnatocin jihohin kasar nan ba zasu iya sarrafa ma’adinan da ke shimfide a jihohin su ba.

Ministan ma’adanai da bunkasa Tama da karafa, Olamilekan Adegbite, ne ya bayyana hakan a wani taron wayar da kai da ya hadar da kwamishinonin shari’a dana ma’adanai da  muhalli na shiyyar Arewa ta tsakiya da suka gudanar a Abuja

Adegbite ya kuma ce ana amfani da kudaden da ake samu daga wani sashe na man fetur a kasar nan don cigaban Najeriya baki daya.

Ya kuma ce yanzu haka Najeria hankalin ta ya fara karkata ga bunkasa bangaren ma’adanai domin samar da kudaden shiga don amfanin kasar nan yadda ya kamata.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 333,342 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!