Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

An gurfanar da matashin ake zargin ya banka wa gida wuta a Gayawa

Published

on

Yan sanda sun gurfanar da matashin nan Salisu Idris a gaban kotun majistret mai lamba 11 da ke sakatariyar Audu Bako a nan Kano.

Sai dai bayan gabatar da shi a gaban kotun ne ya musanta zargin da ake yi masa  na aikata kisan kai sanadiyyar wutar da suka kunna a gidan wani mutum da iyalansa a unguwar Gayawa da ke yankin karamar hukumar Ungogo.

Wanda ake tuhumar Salisu Idris mazaunin unguwar ta Gayawa, ya shaida wa alkalin cewa, tabbas sun je gidan amma ba shi ne ya kunna wutar ba.

A Satin da ya gabata ne dai rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta cafke matashin inda kuma ya amsa cewa shi da wani mutum ne suka je gidan marigayin kuma wancan din ne ya watsa fetur tare da banka wa gidan wuta.

Sai dai Alkalin kotun mai shari’a Usaini Rabi’u ya dage cigaba da sauraron karar a ranar 28 ga wannan wata na Oktoba da muke ciki.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!