Labarai
An haramta kafa hanyoyin sadarwa a jihar Zamfara -CP Ayuba Elkanah
Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta haramta kafa hanyoyin sadarwa na internet ba tare da izini ba, domin inganta tsaro a jihar
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ayuba Elkanah, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya kira a Gusau.
Elkanah, ya ce bayanan da ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro suka samu sun tabbatar da cewa wasu mutane da kungiyoyi basa kiyaye matakan da hukumomi suka dauka don magance ayyukan ‘yan bindiga a jihar.
Ya ce hukumomin tsaro sun bankado wasu mutane da kungiyoyin da ba’a ba su izini ba, kuma suna kafa hanyoyin sadarwa na internet a gidajensu da wuraren kasuwancinsu inda ake zargin ‘yan bindiga suna amfani da su.
Wannan na zuwa ne makwanni uku bayan dakatar da duk wata hanyar sadarwa ta wayar hannu a jihar da Hukumar NCC ta yi da nufin takaita sadarwa tsakanin ‘yan bindiga da ke addabar su.
You must be logged in to post a comment Login