Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Tsaro: Buhari ya bada umarnin rufe hanyoyin sadarwa a jihar Zamfara

Published

on

Gwamnatin tarayya ta bada umarnin rufe layukan sadarwa a fadin jihar Zamfara, domin bawa jami’an tsaro damar fatattakar ‘yan ta’addan da suka damu jihar.

Hakan na zuwa ne biyo bayan bukatar hakan da gwamnatin jihar ta yi, ta cikin wata takarda data aikewa kamfanin sadarwa na kasa NCC a ranar 31 ga watan Agustan da ya gabata.

Tsaro: muna buƙatar gwamnatin tarayya ta kawo mana ɗaukin gaggawa – Majalisar dokokin Zamfara

Inda a jiya juma’a 03 ga watan Satumba shugaban hukumar Farfesa Garba Umar Danbatta ya sanyawa takardar hannu.

Hakan ya sa NCC ta bawa kamfanonin umarnin dakatar da hanyoyin sadarwa a baki dayan jihar daga jiya juma’a 3 ga watan Satumba zuwa 17 ga watan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!