Labaran Kano
An horar da daliban Aminu Kano yadda ake gudanar da aikin Hajji
Shugaban sashen Addinin musulunci na kwalejin ilimi da koyar da nazarin shari’a ta Aminu Kano, Malam Shehu Dahiru Fagge yayi kira ga dalibai da su zage dantse wajen samar da hanyoyi da zasu bunkasa musu harkokin karatu.
Malam Shehu Dahiru Fagge ya bayyana haka ne lokacin da ya jagoranci dalibai zuwa sansanin Alhazai dake nan Kano domin koyar da su yadda ake gudanar da aikin hajji.
Ya ce aikin hajji na daya daga cikin rukunan addinin musulunci, hakan ya sanya suka shirya wannan horo don kara musu fahimta a wannan bangare.
Ya kara da cewa sun shirya wannan bita ne domin su karawa dalibansu kwarin gwiwa akan karatu da suke koya musu a makaranta.
Daga cikin daliban da suka halarci horon sun bayyana jin dadin su game da ilmin da suka koya.
Wakilin mu Shamsu Da’u Abdullahi ya ruwaito cewa Kwalejin ilimi da nazarin sharia’a ta Aminu Kano da aka fi sani da Legal ta shirya horon da nufin wayar da kan daliban sashen hanyoyin gudanar da aikin Hajji.