Addini
An Ja Hankalin Al’ummar Musulmi Kan Kiyaye Iyakokin Allah
Na’ibin limamin masallacin Juma’a na Sahaba Dakta Abdullahi Muhammad Getso ya ja hankalin al’ummar musulmi kan kiyaye iyakokin Allah a cikin rayuwar su.
Dakta Abdullahi Muhammad Getso ya bayyana hakan ne ta cikin hudubar Idin Sallah karama da ya gabatar a masallacin na Sahaba dake unguwar Kundila a birnin Kano.
Ya ce ya zama wajibi musulmi musamman matasa su ci gaba da siffantuwa da halaye na kwarai da suka siffanta dasu a cikin watan Ramadan da ya gabata don inganta rayuwar su, tare da kaucewa abota da wadanda tarbiyyar su ta saba koyarwa addinin musulunci da kuma al’adar mutanen wannan yanki.
Na’ibin limamin ya kuma kara da cewa, ya zama wajibi ga shugabanni su zage dantse wajen sauke nauyin da suka dauka na jagorantar al’umma ba tare da nuna wariya ko bambamci ba don shakka babu shugabanci abin tambaya a ranar kiyama.
Dakta Abdullahi Muhammad Getso ya hori iyaye su kula da tarbiyya ‘ya’yan su musamman a wannan lokaci na bukukuwan Sallah.