Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

Rahoto : Al’umma su dage wajen yada ilimin addinin musulunci – Bin Usman

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Sahaba dake unguwar Kundila cikin karamar hukumar Tarauni anan birnin Kano Sheikh Muhammad Bin Usman ya ja hankalin al’ummar musulmi wajen dagewa kan yada ilmin addinin musulunci a yankunan karkara.

Sheikh Muhammad Bin Usman ya bayyana hakan ne ta cikin Hudubar Sallar Juma’a da ya gabatar a masallacin kan darussan dake kunshe cikin kalandar musulunci.

Ya ce shakka babu akwai bukatar sadaukar da kai wajen dabbaka addinin musulunci da kuma koyi da darussan dake cikin kalandar Hijra.

Muhammad Bin Usman ya kara da cewa, ya zama wajibi a baiwa bangaren koyi da magabata na kwarai fifiko ba wai kawai tuna abin da suka yi ba.

Wakilin mu Umar Idris Shuaibu ya ruwaito Hudubar Sallar Juma’ar ta yau da limamin masallacin Sahaba dake Kundila ya gabatar, ta maida hankali kan muhimmancin watan Muharram dake zaman na farko a musulunci.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!