Labaran Kano
An jima ana neman dalibai mata: BUK
Mataimakin shugaban jami’ar Bayero ta Kano mai kula da sha’anin mulki, Farfesa Haruna Wakili, ya bayyana cewa tursasa wa dalibai ta hanyar neman su da ake zargin wasu daga cikin malamai na yi da sunan baiwa daliban maki ba sabon abu ba ne a sassan duniya.
Farfesa Haruna Wakili, ya bayyana haka ne ta cikin shirin’’Duniyar mu a Yau na nan Freedom Radio, da ya mayar da hankali kan irin yadda ake haike wa dalibai a makarantu.
Ya ce ana samun irin wannan mummunar ta’ada a sassan da suka hadar da manyan makarantu da kamfanoni da sauran fannoni da dama.
Ita kuwa mataimakiyar shugaban jami’ar Yusuf mai Tama Sule, Dr. Amina Salihi Bayero, ta bayyana cewa dalibai ma na da tasu matsalar wajen kara ta’azzara lamarin bisa yadda basa kai korafin malaman da suka neme su da aikata badalar.
Da take yin tsokaci ta cikin shirin, kwararriyar lauya daga kungiyar lauyoyi mata ta duniya FIDA, Barista Amina Umar Usaini, cewa ta yi suna samun korafe-korafe da dama daga wajen ‘yan uwan wadanda aka yi yunkurin ciwa zarafin.
Shi kuwa Dr. Mukhtar Ibrahim Bello daga kwalejin fasaha ta jihar Kano, ya bayyana cewa a binciken da makarantar ta yi ta gano akwai dalibai da dama da suke kai kansu ga malamai sakamakon rashin kokarinsu wajen karatu.
Da yake nasa jawabin, jami’in hulda da jama’a na kwalejin ilimi ta gwamnatin tarayya da ke nan Kano Dr. Auwal Mudi Yakasai ya bayyana cewa, cakuda darussa da yawa a manhajar koyarwar kasar nan na daga cikin manyan hanyoyin da ke haifar da irin wannan matsala a makarantu.