Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An kama matashi da ke sojan gona cewa shi mataimakin kwamishinan ƴan sanda ne

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta kama wani matashi da ake zargin yana sojan gona, inda ya ke bayyana kansa a matsayin mataimakin kwamishinan ƴan sanda.

Hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a daren ranar laraba.

Sanarwar ta ce wanda ake zargin mai suna Muhammad Aliyu mazaunin unguwar Mariri ne, inda yaje wani Otal da sunan shi mataimakin kwamishinan ƴan sanda ne a Kano, a don haka ya naso ayi masa ragi su bashi dakin kwana da zai sauki bakinsa.

Sanarwar ta kara da cewa wanda ake zargin ya shaidawa masu Otal din cewa baturan ƴan sandan karamar hukumar Nasarawa ma kaninsa ne.

Kazalika ta cikin sanarwar rundunar ta ce a binciken da ta fara gudanarwa ta gano cewa, wanda ake zargin yana amfani da sunan Ibrahim Muhd Tijjani na bogi a matsayin shi kwararran Likita ne, kuma yana rubutawa marasa lafiya magani su yi amfani da shi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!