Connect with us

Kiwon Lafiya

An kama wasu yan kunar bakin wake a kauyen Mushemiri a jihar Borno

Published

on

Sojojin da ke aiki a rundunar Operetion Lafiya Dole sunkama ‘yan kunnar bakin wake mata su 2 a kauyen Mushemiri dake karamar hukumar Konduga a jihar Borno.

Wannan na kunshe cikin sanarwar da rundunar sojan kasar na ta buga a shafin ta na Twitter cewa, matan da ake zargin ‘yan kunnar bakin wake ne, suna yunkurin kai hari tare da tada bom a bataliya ta 222 na rundunar sojan kasar nan dake yankin na Konduga a daren jiya Laraba.

Haka zalika a cewar sanarwar jami’an rundunar Operation Lafiya Dole sun gano cewa matan sun makale bom din a jikin su, a yayin da suke kokarin tada shi, amma jami’an suka kama su.

Sojojin sun kama su ne a dai-dai lokacin da suke binciken ababan hawa, yayin da ‘yan kunnar bakin waken suke yunkurin kai harin da misalin karfe 9 da rabe na daren jiya Laraba.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,926 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!