Kiwon Lafiya
An kasa cimma matsaya tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar malamai kwalejojin fasaha
Gwamnatin tarayya da kungiyar malaman kwalejojin fasaha ta kasa ASUP sun kasa cimma matsaya a taron da suka gudanar a jiya domin lalubo bakin zaren matsalar su da suka ce gwamnati ta ki kula da ita.
Gwamanti da kungiyar ta ASUP sun ki amincewa da bukatun juna, inda kowa ya kafe akan bakan sa ya yin zaman na jiya, lamarin da ya janyo aka dage zaman har zuwa watan janairu mai kamawa
Yayin zaman dai ministan Ilimi Malam Adamu Adamu ne ya wakilici gwamnatin tarayya inda kuma shugaban kungiyar ta ASUP Usman Dutse ya jagoranci kungiyar.
Da yake jawabi jin kadan bayan kammala zaman ministan ilimi Malam Adamu Adamu ya ce duka bagarorin biyu sun tashi ba tare da cimma wata matsaya ta azo a gani ba.