Connect with us

Kiwon Lafiya

Hukumar INEC ta ce tana aiki ka’in da-na’in wajen inganta zaben badi

Published

on

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta ce, tana aikika’in-da-na-in wajen gudanar da shirye-shiryen babban zaben badi ingantacce,karbabbe kuma sahihi.

Shugaban hukumar zabe ta kasa INEC ne ya bayyana hakan a babban taron masu rike da masarautun gargajiya karo na 5 mai taken’’ Yawan fama da rashin tsaro a cikin shekarar zabe’’ da aka yi a jiya Laraba a jihar Kaduna.

Farfesa Mahamod Yakubu ya ce ‘yan siyasar kasar nan basa yin dumokuradiyya a aikace kuma sune ummul-aba-isin wajen kawo tarnaki kan rashin cigaba a harkokin dumokuradiyya a Najeriya, ganin yadda suke sauya sheka daga wannan jam’iyyar zuwa wata.

Haka zalika shugaban hukumar zaben INEC yace hukumar ba zata yi kasa a gwiwa ba wajen cigaba da gudanar da shirye-shiryen tunkarar babban zaben na badi.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,834 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!