Connect with us

Kiwon Lafiya

Yan tada kayar bayan yankin Bakassi sun ajeye makamai

Published

on

Yan daban yankin Bakassi da ke jihar Cross River sun ajiye makaman su, kuma sun mika kansu ga gwamnati, bisa alkawarin sun tuba za kuma suma yan kasa nagari masu bin doka da oda.

Shugaban gungun yan dabar Simply Benjamin ya jagoranci mika kan na su ga gwamnati a kauyen Ikang da ke karamar hukumar Bakassi cikin shirin yin afuwa ga yan daban da  wamnan jihar Ben Ayade yayi ga wadanda suka tuban da ya gudana jiya.

Ya ce shirin afuwar da aka yi musu ba karamin abin tarihi ne ga al’ummar yankin ta Bakassi ba, in da ya ce gwamanti ta yi nasarar dakile fitin tunu a yankin su kuma suniyi nasarar samun yancin su.

Simply Benjamin ya ce wannan ya samu ne sakamakon rawar da masu ruwa da tsaki suka taka a yankin na aiki ba dare ba rana wajen kawo karsehn fitintinun da ke faruwa a yankin

Da yake jawabi bayan kaddamar da shirin yin afuwar gwamnan jihar Ben Ayade, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta kula da walwalar tubabbun yan daban, inda ya ce jihar ita kadai ba zata iya kula das u baki daya ba.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,589 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!