Connect with us

Labarai

An kawo Rukuni na biyu na ƴan Najeriya 705 da ke gudun hijira a Kamaru

Published

on

Rukuni na biyu na ’yan kasar nan 705 da ke gudun hijira a ƙasar Kamaru sun dawo gida, inda suka isa garin Banki a Karamar Hukumar Bama ta Jihar Borno.

 

Wannan na cikin sanarwar da Mai Magana da Yawun Gwamnan Jihar Borno, Dauda Iliya, ya fitar.

 

Ya ce an dawo da ’yan gudun hijirar ne daga birnin Maroua na Jamhuriyar Kamaru a jiya Alhamis.

 

A cewarsa, dawowar na cikin shirin ci gaba na mayar da ’yan Najeriya da rikicin tsaro ya tilasta musu barin muhallansu, tare da tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da tallafa musu wajen sake zaunar da su su ci gaba da rayuwa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!