Labarai
An kuɓutar da sojan da ƴan bindiga suka sace a NDA

Rundunar tsaron ƙasar nan ta samu nasarar kuɓutar da sojan nan da ƴan bindiga suka yi garkuwa da shi.
Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Manjo CL Datong ne tun a ranar 24 ga Agustan 2021 a Kwalejin horar da sojoji NDA a Kaduna.
Tun bayan sace shi ne babban hafsan tsaro shiyya ta 1 ya ba da umarni ga jami’an tsaro da su tabbatar an kuɓutar da shi.
Jami’an tsaron sun yi nasarar kuɓutar da shi a ranar 17 ga watan Satumba da muke ciki bayan wata musayar wuta da ƴan bindiga a yankin Afaka da ke Birnin Gwari a jihar Kaduna, lamarin da basu nasarar ceto shi.
Cikin wata sanarwa da mataimakin mai magana da yawun rundunar tsaro shiyya ta 1 Kanal Ezindu Idimah ya fitar ta tabbatar da kuɓutar sa, sai dai ya ce yayin musayar wutar jami’in sojin ya samu rauni.
You must be logged in to post a comment Login