Labarai
An naɗa Alhaji Muhammad Barau a matsayin sabon sarkin Sundan na Kontagora

Gwamnatin jihar Neja ta amince da naɗin Alhaji Muhammad Barau a matsayin sabon sarkin Sudan na Kontagora.
Kwamishinan ƙananan hukumomi da harkokin masarautu na jihar Emmanuel Umar ne ya sanar da hakan.
Ya ce, tun a ranar 19 ga watan Satumbar da ya gabata ne masu naɗin Sarki a masarautar Kontagora suka aike wa Gwamnati zaɓin da suka yi.
Daga nan ne kuma Gwamnann jihar Abubakar Sani Bello ya amince da naɗin.
A watan Satumban da ya gabata ne marigayi Sarkin Sudan na Kontagora Alhaji Sa’idu Umaru Namaska ya rasu, bayan shafe shekaru 47 yana mulki.
You must be logged in to post a comment Login