Labarai
An nada Gwanaye a haddar Al’kur’ani a Kano
Wani Malami a Jami’ar Bayero ta Kano Sheikh Dr. Aliyu Haruna Muhammad yace watsi da koyarwar addinin Musulunci da kuma shagaltuwa da mutane suka yi wajen neman duniya mai makon neman Ilimin Addini na daga cikin abunda ke jawo matsalolin da ake fuskanta a yanzu.
Dr. Aliyu Muhammad ya bayyana hakan ne lokacin bikin nadin Gwani Idris Abdussalam Mai Haniniya Koki da Mahaifinsa a matsayin Gwanaye a haddar Al’kur’ani wanda suka shafe shekaru masu yawa suna yiwa Al’kur’ani hidima wanda aka gudanar a unguwar Koki.
Ya kara da cewa “la’akari da irin yadda mutane a yanzu basu fiya baiwa neman Ilimin Addini Musulunci muhimmanci ba musamman ‘ya ‘yansu wanda hakan ke sanya ‘ya’ya basa ganin girman iyayensu suma iyaye basa darajta ‘ya’yansu saboda basuda cikakken ilimin Addinin Musulunci da sunna Annabi “
A nasa bangaren Gwani Idris Mai Haniniya bayyana jin dadinsa yayi da wannan rana.
“In da ya shawarci ‘yan uwansa matasa dasu tashi tsaye wajen neman Ilimin Addinin Musulunci, yana mai cewa kamata yayi mutane su rungumi koyarwar Al’kur’ani domin itace kadai mafita duniya da lahira”
Wakilin Mu Abdulkarim Muhammad Tukuntawa daya halarci taron ya shaida mana cewa mutane da dama ne suka halarci taron nadin ciki harda malamai daga tsangayun koyarda karatun Al’kur’ani daga gurare daban daban da sauran malamai a fadin jihar Kano.
You must be logged in to post a comment Login