Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Rashin kyautatawa almajirai shi yasa suke samun kalubale- Muhammad Tahar

Published

on

Kwamishinan kula da harkokin Addini na jihar Kano, Malam Muhammad Tahar Adamu yace Almajiranci dadaddiyar hanya ce ta koyar da ilimin Addinin Musulunci.

Malam Muhammad Tahar ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Duniyar mu a yau da ya mayar da hankali kan matsayar da gwamnonin Arewacin kasar nan suka cimma kan gyara tsarin da ake gudanar da Almajiranci.

Malam Muhammad Tahar Adamu  yace, neman ilimi wajibi ne sai dai yadda aka mayar da neman sa a yanzu ya saba ka’ida, hakan ne ya sa gwamnonin arewacin kasar nan suka mayar da hankali kan yadda za su shawo kan matsalar, ta hanyar samar da kwamitin da zai tantance makarantun tsangayu da ke jihar Kano.

Ya kuma ce, Gwamnati ta yanke hukuncin mayar da almajirai jihohin su na asali, la’akari da mafi yawa daga cikin almajiran ba ‘yan asalin jihar Kano bane, yayin da itama jihar Kano aka dawo mata da almajirai 956 daga makwabtan jihohi.

Kwamishinan na harkokin Addinai na jihar Kano Malam Muhammad Tahar Adamu, ya kuma musanta cewar ana so a mayar da tsarin Almajirci tsarin wani Addini daban, inda ya ce gwamnati ta lura da yadda Almijirai ke watangaririya a gari tare da rashin makoma wanda hakan ke sawa su shiga gurbatacciyar rayuwa.

Ganduje zai fara gurfanar da iyayen almajirai masu bara a gaban kotu

Gwamna Badaru ya dinkawa Almajirai kayan sallah

A nasa bangaren tsohon Kwamishinan ilimi na Jihar Kano, kuma shugaban gidauniyar kyautata rayuwar Almajirai a jihar Kano Malam Hassan Yusuf, ya ce, rashin kyautata harkar Almajiranci tun da fari shi ya janyo a yanzu ake fuskantar kalubale.

Ya kara da cewa, iyayen da ke tura ‘ya’yan su almjiranci basa bibiyar sha’anin karatun su, wanda hakan ke baiwa malamai tilasta su neman kudi don su dauke bukatun kan su, ya kuma ce akwai gyara kan yadda gwamnati ta tasamma gyara sha’anin Almajirci ba tare da shawartar masana harkar ba.

Dukkanin bakin sun karkare da kira ga iyaye da su rika daukar dawainiyar yaran su yayin da suke neman ilimi, wanda hakan zai taimaka wajen rage shiga halin matsi da yaran ke shiga.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!