Labarai
An nemi Kotu ta hana ɗaukar hoton Ɗan Chinan da ake zargi da kisan Ummita
Lauyan da ke kare Ɗan Chinan nan Mista Geng Quanrong, Barista Muhammad Balarabe Ɗan’azumi ya nemi Kotu ta hana ɗaukar hoton wanda yake karewa.
Ya ce, hakan tozartawa ce ga wanda ake zargi.
Sai dai mai shari’a bai ce komai ba kan wannan buƙata.
Wannan dai ya biyo bayan da lauyan Gwamnati Barista Musa Abdullahi Lawan ya nemi Kotu ta hana a riƙa ɗaukar hoton wanda yake yiwa Ɗan Chinan fassara.
Lauyan ya ce, ɗaukar hoton nasa tamkar keta mutunci ne, domin ba zarginsa ake ba, hassalima aro shi aka yi daga ofishin jakadancin ƙasar China.
Mai shari’a Sanusi Ma’aji ya amince da buƙatar lauyan Gwamnati inda ya hana sake ɗaukar hoton wanda yake fassarar.
You must be logged in to post a comment Login