Labarai
An sace mutane 2000 tare da kashe 1500 a watanni 4 farkon 2025-NHRC

Hukumar kare haƙƙin Bil-adama ta kasa NHRC, ta ce tsakanin watan Janairun shekarar da ta gabata zuwa Afrilun wannan shekarar da muke ciki an sami aukuwar sace-sacen jama’a kusan 2000, ya yin da kuma aka halaka wasu kusan 1, 500 a sassan kasar.
Ta cikin rahoton da hukumar ta fitar ta ce an sace sama mutum 1,712 tare da kashe mutum 1, 463 a wurare daban-daban a fadin kasar nan, daga watan Janairu shekarar da ta gabata zuwa watan Afrilun bana lamarin ya nuna karuwar ayyukan ta’addanci musamman yankin Arewacin kasar nan.
Kwamared Kamal Adam shi ne sakataren kare hakkin Bil’adama ta kasa reshen Jihar Kano ya tabbatar da alkaluman rahotan a tattaunawarsa da Freedom Radio.
Manjo Muhammad Lawal Yaqub ,Mai ritaya Masani ne kuma mai sharhi kan lamuran tsaro a kasar nan ya ce Lokaci ya yi da za a fara samo tushen dalilan ci gaba da Afkuwar hakan.
A cewar Kwamred Bello Basi Fagge, rahoton bai zo da mamaki ba ganin yadda matsalar tsaro ta zama wata babbar Sana’a ga wasu marasa aikin yi a kasar nan.
Matsalar sace sacen mutanen de ta fi kamari a yankin arewacin kasar nan musamman ma yankin arewa maso Yamma, a jihohin Katsina , Kaduna , Zamfara , Sokoto da Kebbi , sai na ‘yan tada kayar baya a Arewa maso Gabas ,daga Adamawa zuwa Yobe da Borno.
Kalubalen da al’umma ke ci gaba da kiraye-kiraye ga hukumomi da su dauki matakin dakile matsalar.
You must be logged in to post a comment Login