Labarai
An saki Kason farko na sunayen daliban da suka shiga makarantun hadaka na gwamnatin tarayya
Gwamnatin tarayya ta saki kason farko na sunayen daliban da suka samu nasarar shiga makarantunta na hadaka.
Wannan na zuwa ne kwanaki uku bayan da ta karbi sakamakon jarabawar daliban da suka yi don neman shiga makarantun.
Ta cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai na ministan ilimi malam Adamu Adamu, Ben Bem Goong ya sanyawa hannu, na cewa a ranar larabar da ta gabata ne gwamnati ta mika da sakamakon jarabwar ga shugabannin makarantun da ke fadin kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login