Connect with us

Labarai

An sako abokin marigayi tsohon babban hafsan Najeriya da aka yi garkuwa da shi

Published

on

Wanda ake zargi da kashe tsohon babban Hafsan tsaron kasar nan marigayi Air Chief Marshal Alex Badeh mai ritaya ya sako abokin marigayin bayan garkuwa da yayi da shi.

Rahotanni sun bayyana cewar, sai da iyalan abokin kuma shakiken marigayi Alex Badeh suka biya kudin fansa na miliyoyin Naira kafin a sake shi.

A makon jiya ne rundunar ‘yan sanda ta kasa ta bayyana cewar, marigayin ya sami munanan raunika sakamakon harben binding da ya samu da yayi sanadiyar  mutuwar sa, yayin da direban sa ya sami munanan raunika bayan da aka sace abokin marigayin daga bisani.

Haka zalika rahotanni daga rundunar ‘yan sanda ta kasa ta   bayyana cewar, kafin kai hari tare da kashe Alex Badeh a kan hanyar Abuja zuwa Keffi sai da aka kai irin makamancin wannan harin a watan jiya har sau 2 a dai kan hanyar Abuja zuwa Keffin.

Haka zalika wata majiya ta bayyana cewa, rundunar sojan kasar nan zata gudanar da taro da rundunar ‘yan sanda ta kasa bayan an dawo daga hutun bikin Kirsimeti.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,290 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!