Labarai
An sako iyalan ɗan majalisar da aka sace a jihar Bauchi
Matan dan majalisar mai wakiltar ƙaramar hukumar Dass a jihar Bauchi Musa Baraza da ƴar sa ɗaya da masu garkuwa da mutane suka sace sun shaki iskar ‘yanci.
A ranar Alhamis da ta gabata ne wasu da ba a san ko su wanene ba suka yiwa dan majalisar kisan gilla tare da tafiya da matan sa biyu da ƴar sa ɗaya a gidan sa da ke ƙaramar hukumar Dass.
Matan ɗan majalisar sun hada da Rashida Musa Mante mai shekaru 40 da Rahina Musa Mante mai shekaru 35 sai kuma ƴar sa Kausar Musa Mante mai shekara ɗaya a duniya.
Hakan na cikin sanarwar da shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar Bauchi Dakta Ladan Salihu ya wallafa a shafin sa na Twitter.
Ta cikin sanarwar ya bayyana cewa tuni gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammad ya baiwa likitoci da jami’an tsaro umarnin kula da iyalan gidan ɗan majalisar don tabbatar da kwanciyar hankulan su.
Kazalika rundunar yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da dawowar iyalan dan majalisar bayan da masu garkuwa suka sace su.
You must be logged in to post a comment Login