Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yadda ‘yansada suka yi ram da daya daga cikin matasan da ake zargi da yankewa yarinya matunci a Bauchi

Published

on

An kama daya daga cikin matasan da suka yi wata yarinya aika-aika a Jama’aren jihar Bauchi kafin  tawagar gwamnatin jihar ta zo nan Kano a jiya Lahadi.

Hakan yasa muka tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Bauchi DSP Ahmad Mohammed Wakili.

“Yace tuni hukumar ‘yan sandan Jihar Bauchi ta baza mutanen ta don nemo wadanda suka aikata wannan ta’asa Kuma yanzu haka sun Sami nasarar kama mutum daya daga ciki mai suna Adamu Abdul’aruf mai kimanin shekaru ashirin”

A cewar DSP Ahmad Mohammed  dayan da ake zargin sun aikata wannan mumunan aika-aika  ya tsere.

Kuma a jiya Lahadi ne Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya aiko da tawaga ta mussaman da ta wakilci shi zuwa asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano dake nan Kano don ganin halin da yarinyar ke ciki.

Abdulzak Nuhu Zaki kwamishinan kananan hukumomin Jihar Bauchi shi ne ya jagoranci tawagar kuma yace yanzu haka an kama wasu daga cikin wadanda suka aikata wannan ta’asa.

Hon. Abdulzak Nuhu Zaki yana mai cewa “Gwamnatin Jihar Bauchi ta yi alkawari za ta dauki nauyin biyan kudin aikin da za’a yiwa Hauwa”.

Ana  dai zargin wasu matasa biyu da yankewa wata yarinya mai suna Hauwa ‘yar kimanin shekaru shida matancin ta.

Wannan al’amarin ya faru ne a garin Jama’are dake jihar Bauchi a ranar Larabar makon da ya gabata.

Wakiliyar mu Hadiza Ado Jinta da ta ziyarci asibitin Malam Aminu Kano ta zanta da
Hafsatu wadda ita ce marikiyar yarinyar kuma yayar mahaifin yarinyar ta bayyana yadda abun ya faru.

“Ta ce ta dumama ruwan zafi zata yi musu wanka sai suka fita, fitar su ke da wuya sai  suka hado da matasan ya yin da suka tambaye ko kun san gidan Suraja daga nan ne suka umarce su da su je wani Kango daga nan ne kuma yar uwar ta ta tsare, bayan nan ne suka kwantar da ita suka yanke Matuncin ta daga aka dauke ta zuwa asibiti”

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!