Labarai
An sako masu bauta 38 da aka sace a cocin Kwara da ke Najeriya

An sako Masu bauta 38 da aka sace a cocin Kwara da ke ƙaramar hukumar Eruku a baya baya nan, a harin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum uku tare da jikkatar wani guda.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙaramar hukumar Ekiti, Dada Sunday ya fitar a daren jiya Talata, ya tabbatar da cewa gwamnan jihar, AbdulRahman AbdulRazaq ne ya miƙa waɗanda aka ceto ga shugaban ƙaramar hukumar Ekiti, Awelewa Olawale Gabriel, a birnin Ilorin.
Da yake karɓar wadan da aka ceto, Awelewa ya bayyana godiya rsa ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da gwamna AbdulRazaq da duka hukumomin tsaro bisa gaggawa da ƙoƙari wajen ceton mutanen.
Ya ce aikin haɗin gwiwar jami’an tsaro da gwamnati ya taimaka wajen kammala ceto cikin lokaci, tare da ba wa wanɗan da aka kubutar cikakkiyar kulawa, haka zalika sanarwar ta ce tawagar waɗan da aka ceto ta isa garin Eruku da misalin ƙarfe 6:30 na yammacin Talata.
You must be logged in to post a comment Login