Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An samar da cikakken tsaro a jihohin da za’ayi zaben gwamnoni: Ribado

Published

on

Mai bai wa shugaban Kasar Nijeriya shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya ce ansamar da ingantaccen tsaro ga jihohin Kogi, Beyalsa da kuma Imo a dai-dai lokacin da ake ci gaba da shirye-shiryen gudanar da zaben gwamnan a jihohin a yau Asabar.

Cikin wata sanarwar da ofishinsa ya fitar, ya ce gwamnatin tarayya ta kammala duk wani shiri da ake buƙata don gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali da lumana.

Ribado ya gargaɗi ‘yan siyasa kan ƙoƙarin tayar tayar da zaune tsaye, tare da kira ga jami’an tsaro da su gudanar da aikinsu cikin ƙwarewa a lokacin aikin.

Sanarwar ta ƙara da gargaɗin cewa za a samar da tawagar masu sanya idanu a zaɓen domin tattaro bayanan hujjojin tayar da hargitsi ko take dokokin zaɓen.

Rahoton: Yusuf Sulaiman Ahmad

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!