Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An sanya Naira miliyan 10 kuɗin siyan takardar tsayawa takarar Chairman

Published

on

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano, KANSEIC, ta sanya Naira miliyan 10, a matsayin kudin tsayawa takarar shugabancin ƙaramar hukuma, yayin da kowane mai neman takarar Kansila zai biya Naira miliyan 5.

Shugaban hukumar zaben na jihar, Farfesa Sani Lawan Malunfashi, ne ya bayyana hakan yau a ofishin hukumar, yayin da yake ƙaddamar da jadawalin zaɓen da kuma ka’idojin da aka tsara ga shugabannin jam’iyyu na jihar Kano, da kuma zauren gammayar hadin kan jamiyun kasar nan.

Da yake jawabi jim kaɗan da kammala taron amadadin shugaban hukumar kwamishina mai kula da tsaro da tsare-tsaren hukumar Shehu Na-All… Kura, ya ce an sanya Naira miliyan goman ne a matsayin kuɗin tsayawa takarar shugabancin ƙaramar hukumar, yayin da mai neman takarar Kansila zai biyar Naira miliyan biyar, duba da halin matsin rayuwar da aka samu kai a ciki.

Ya kuma ce hukumar zaɓen ba za ta lamunci karya doka ko kuma cin mutumcin juna, ko tayar da hargisti ba yayin zaben ƙananan hukumomin jihar Kano da za’a gudanar.

A nasa ɓangaren mataimakin sakataren jam’iyar PRP, ta jihar Kano Alhaji Musa Mai gari, ya ce akwai buƙatar hukumar ta rage kuɗin Form, ɗin tsayawa takarar kasancewar sun yi yawa sosai bisa halin tsadar rayuwar da ake ciki.

Sai dai kuma a nasa ɓangaren shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Kano, Hashim Sulaiman Dungurawa, ya ce sun gamsu da kuɗin da hukumar ta sanya na Naira miliyan goma a matsayin kuɗin tsayawa takarar shugabancin ƙarama, wanda kuma masu neman Kansila za su biya Naira miliyan biyar.

Sai dai kuma yayin da yake jawabi a lokacin taron mai magana da yawun jam’iyyar NNPP, ta jihar Kano Musa Nuhu Ƴan Kaba, ya bukaci hukumar da ta rage wani abu kan Naira miliyan goma da ta sanya a matsayin kuɗin tsayawa takarar shugabancin ƙaramar hukuma, a cewar sa kuɗin ya yi yawa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!