Connect with us

Labarai

An sauyawa tsohon Sarkin Kano wuri a jihar Nasarawa

Published

on

An kammla yarjenjeniyar kan sauyawa tsohon Sarkin Kano malam Muhammadu Sunusi na II daga kauyen Loko zuwa karamar hukumar Awe a jihar Nasarawa.

Tsohon shugaban ma’aikata na fadar sarkin Kano Munir Sanusi ya tabbatar da hakan ga jaridar Daily Nigerian cewa sun isa fadar gwamnatin jihar Nasarawa don sauya musu matsuguni dag kauyen Loko zuwa karamar hukumar Awe.

Kwamshinan ‘yan sand ana jihar ta Nasarawa Bola Longe da takwaran sa na farin kaya na fadar gwamnatin ta jihar Nasarawa don karbar tsohon sarkin Kano malam Muhammadu Sanusi na II.

Yanzu-yanzu: Ganduje ya tsige sarki Sanusi II

Majalisar dokokin Kano ta tsige shugaban masu rinjaye

Talakawa sun yi Al-kunuti kan yunkurin tsige Sarkin Kano

Jaridar ta DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa, mai yuwa ne wasu daga cikin masu fada aji sun sanya baki wajen sauyawa sarkin wuri ciki akwai Aliko Dangote da dai sauran su.

A cewar, Jaridar karamar hukumar Awe ya fi abubuwan more rayuwa akan kauyen Loko dake jihar ta Nasarawa.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 335,226 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!