Connect with us

Labarai

An tashi baram-baran a taron APC bayan kin ambatar sunan Shettima a tazarcen Tinubu

Published

on

Rikici ya barke a wani taron jiga-jigan jam’iyyar APC na yankin Arewa maso Gabas da aka gudanar a yau Lahadi a jihar Gombe, bayan da mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙasa mai kula da yankin, Comrade Mustapha Salihu, ya kasa ambaton sunan mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima yayin da yake goyon bayan shugaba Bola Ahmed Tinubu domin zarcewa wa’adi na biyu.

 

Taron dai ya samu halartar kusan dukkan ministoci, ‘yan majalisa da gwamnonin jam’iyyar daga yankin, ciki har da shugaban jam’iyyar APC na ƙasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya jagoranci wasu fitattun ‘yan siyasa zuwa taron.

 

A lokacin da Salihu ya samu damar yin jawabi, ya bayyana goyon bayansa ga shugaban ƙasa Tinubu a matsayin wanda ya kamata ya fito ba tare da hamayya ba a zaben fidda gwani na jam’iyyar, amma bai ambaci mataimakinsa Kashim Shettima ba, wanda shi ma dan yankin Arewa maso Gabas ne.

 

Bayan kammala jawabinsa, mahalarta taron sun fara zagi da caccakar Salihu, wasu ma suna barazanar kai masa hari, lamarin da ya tilasta jami’an tsaro fitar da shi daga wajen taron domin kare lafiyarsa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!